Mata masu digiri sun koma sana’ar kabu-kabu a Abuja

0
115

Shirin Rayuwata na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda wasu mata da suka kammala karatun digiri a Najeriya suka rungumi aikin tukin tasi ko kuma kabu-kabu musamman a birnin Abuja.

Sai dai matan sun shaida wa RFI Hausa irin kalubalen da suke fuskanta kamar yadda wasu mazan ke neman lalata da su.

Matan masu aikin kabu-kabun a birnin Abuja sun ce, sana’ar ta karbe su domin kuwa suna samun kudi mai yawan gaske da suke amfani da shi wajen tallafa wa iyalansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here