Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa a tarayyar Najeriya ta sanar da nasarar kwato yara biyu cikin guda 6 ‘yan makaranta da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a ranar juma’ar da ta gabata.
Idan dai mai saurare zai iya tunawa mun baku labarin yadda ‚yan bindiga suka kutsa kai makarantar Firamare ta garin Alwaza dake karamar hukumar Doma a jihar ta Nasarawa suka yi awon gaba da kananan yara dalibai su 6.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Rahman Nansel ya tabbatarwa da manema labarai cewa kawo yanzu jami’an tsaro na samun bayanai daga daliban da nufin gano hanyoyin da za’a bi wajen kwato sauran yaran da suka rage a hannun ‘yan bindigar.
A cewar sa rundunar hadin gwiwa tsakanin sojoji, ‘yan sanda da kuma ‚yan bijilanti karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sandan jihar Mai yaki Muhammad Baba ne suka kutsa cikin daji sannan suka gano yaran guda biyu dukannin su mata da shekarun su basu wuce 6 ba.