Kamfani na nufin duk wurin kasuwanci ne da mutum ko wasu mutane suka hadu akan wata haja suna kokarin su ga sun gyara ta yadda za’a saya, ta hanyar kamfani ne kasa ke zama lafiya a tattalin arziki kuma idan ka bude Ka taimaki wasu su samu aiki.
Burodi yana daya daga cikin manyan abinci wanda ake yawan ci a fadin duniya ba ma wai a kasar Hausa ba kawai.
A dalilin haka ne kasuwancin Burodi ya na da riba kuma ana samun kudi da shi. kamfanin Burodi yana daya daga cikin kamfanonin da ya kamata ka sani wanda suka ta’allaka da abubuwan bukata yayin bude kamfanin Burodi.
- Jari
- Wurin yi wato kamfanin ma’aikata
- kayan masarufi kamar fulawa
- kayan masarufi kamar su fulawa, Yeast, butter, Suga, gwangwanayen gasawa, rumbun gasawar na da ko kuma na Zamani, hanyar raba Burodin.
Abubuwan da ke taimakawa wajen gina kamfanin
1.Mallakar lambar CAC:A Nijeriya idan kana son bude kamfani mallakar lambar CAC na da matukar amfani gare ka da kuma kamfanin ka saboda kana da shaidar kasuwanci ta kasa.
Inda amfanin haka ya na taimakawa ko da gwamnati ta na son ta ba da wani tallafi ko kuma rance ga masu kamfani ana saurin samu.
2.Rajista da NAFDAC: yanayin kasuwancin Burodi yana karkashin kamfanonin masu abinci dole ne ka biyo ta hanyar Hukuma Mai Kula da Hada Abinci da Magunguna ta Kasa wato NAFDAC don masu sayen kayan ka sun fi jin dadi su ga akan abin akwai wannan lambar sun san gwamnati ta tantance shi.
3.Rajistar da kungiyoyin Burodi:Ya kamata ka hada kai da takwarorinka a cikin harkar kasuwancin wadanda kuke sana’a iri daya.
Hakan Yana taimakawa saboda ko kudi sun karu ko kuma wani ragi za ka sani a nan.
Bayan haka kuma akwai kyaututtuka da kungiyoyi masu zaman kansu suke samu daga wasu ko kuma daga gwamnati musamman idan wata matsala ta samu ana kuma iya samun tallafi a ce sai wadanda suke a ciki ka ga yana da kyau ka yi rajista da ka hadu da su domin samun ci gaba.
Yanayin kasuwancin Burodi:
Akwai matakan kasuwancin daban-daban ne wadansu wanda aka fi yi kuma aka fi samun nasara su ne:
- Daga kamfani zuwa ‘yan talla
- Daga ‘yan talla zuwa masu shayi ko kuma shaguna
- Daga masu shayi ko masu shaguna zuwa masu saye daidai
- Daga masu kamfani zuwa masu saye daidai
Allah ya ba mu sa’a.
LEADERSHIP