Awanni bayan ficewa daga tafiyar Tinubu da APC, Naja’atu Muhammad ta ziyarci Atiku

0
190

‘Yar gwagwarmayar nan kuma ‘yar siyasa a jihar Kano, Hajiya Naja’atu Muhammad cikin awa 72 da ficewa daga jam’iyyar APC tare da kaurace wa siyasar bangaranci ko ta jam’iyya.

Naja’atu, dai ta yi murabus a matsayin daraktan yakin zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu a ranar Alhamis, kwatsam a ranar Lahadi kuma aka ganota ta ziyarci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a Abuja inda ta sha alwashin yin gamayya da shi.

LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa a ranar Alhamis dai Naja’atu ta aike da wasikar ficewa daga APC zuwa ga shugaban kungiyar jam’iyyar na kasa Sanata Abdullahi Adamu inda take bayyana masa dalilanta na yin hakan.

Kazalika bayanai daban-daban sun yi nuni da cewa a ranar Asabar Naja’atu ta ce ta daina siyasar bangaranci ko jam’iyyar illa iyaka za ta kasance mai bin mutum da cancanta. Sai dai ganinta da aka yi da Atiku tamkar yin amai ne da lashewa

 

‘Yar fafutukar ta nuna cewa jam’iyyun siyasa da suke kasar nan gaba daya ba su da manufofi na daban kuma ‘yan siyasa na iya sanya kowace irin riga domin cimma manufarsa ta kashin kai a kowani lokaci.

 

“Shi ya sa muke ganin ‘yan siyasa na shiga wannan jam’iyyar su fita su koma wata,” ta ce.

 

Sai dai LEADERSHIP ba ta iya tabbatar da cewa ko Hajiya Naja’atu din ta shiga cikin jam’iyyar PDP ba zuwa yanzu ko kuma kawai zallar goyon bayan takarar Atiku Abubakar ta ke yi a zaben 2023.

 

A hirarsa da jaridar LEADERSHIP a ranar Lahadi, Kakakin kwamitin yakin zaben Atiku/Okowa, Sanata Dino Melaye ya tabbatar mana cewa Hajiya Naja’atu Muhammad din ta ziyarci Atiku Abubakar a ranar Lahadi da yammaci.

Melaye, wanda aka gano shi cikin hoton ziyarar tare da Naja’atu da Atiku, ya shaida ma wakilinmu cewa ‘yan fafutukar za ta yi magana kan wannan matakin ne a lokacin da ya dace.

LEADERSHIP

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here