Limaman masallatan Juma’a na Arewa sun ayyana goyon bayan su ga takarar Tinubu da Shettima

0
99

Limaman Masallantan Juma’a na daukacin jihohi 19 na Arewacin Nijeriya, sun ayyana goyon bayansu ga takarar Musulmai biyu, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima.

Sun sanar da hakan ne a taron da suka gudanar a Jihar Kaduna, karkashin gidauniyar ‘Al’umma Global Islamic’.

Jim kadan bayan kammala taron, a yau Talata, a tattunawarsa da manema labarai, shugaban kwamitin taron, Sheikh Tajuddeen Imam, ya ce “Babu gudu ba ja da baya kan wannan goyon bayan namu na takarar shugaban kasa ta Musulmai biyu.

“Mun hada wannan taron ne don mu hada kanmu waje daya, mu kuma sanar da matsayarmu kan takarar Musulmai biyu a zaben shugaban kasa na 2023.”

Tajuddeen ya kara da cewa, “Takarar ta Musulmai biyu muke goyon baya, musamman don a kara ciyar da Nijeriya gaba ta fannin inganta tattalin arzikin kasa.

A cewarsa, “Burinmu shi ne masu takarar Musulmai biyu idan sun lashe zaben, dole ne su ja daukacin ‘yan Nijeriya don tafiya tare, ba tare da nuna wariya ga wani jinsi ko Addini ba.

“Muna kuma fatan a kai ga nasara a zaben, za su kara kaimi wajen kirkiro da ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya da kuma kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here