Naira Biliyan N370.7 kachal aka tara a matsayin haraji a cikin shekaru 7 – Emefiele

0
88
Godwin-Emefiele
Godwin-Emefiele

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya yi karin haske kan cece-kucen da ake tafkawa a kan yawan kudaden shiga da ake samu daga kudaden da bankunan kasuwanci ke cirewa yayin hada-hadar kudi a asusun bankuna (stamp duty)

 

Gwamnan babban bankin na CBN ya shaidawa manema labarai a wajen wani taron karawa juna sani na kwamitin kula da harkokin kudi (MPC) a ranar Talata a Abuja, cewa naira biliyan N370.686 ne kacal duk bankunan kasuwanci suka karba daga harajin tsakanin shekarar 2016 lokacin da aka fara karbar harajin zuwa 2022.

Daga cikin adadin kudaden da aka samu, Mista Emefiele ya ce hukumar tattara kudaden shiga ta tarayya FIRS ta raba kudi har naira biliyan N226,451,720,158.88 ga asusun gwamnatin tarayya (FAAC) don biyan kudade ga matakan gwamnati uku.

Bayanan da babban bankin CBN ya fitar, ya nuna cewa yanzu haka abinda ya rage acikin asusun ajiyar kudin ya kai naira biliyan N144,234,595,346.40.

 

Ku tuna cewa dan majalisar tarayya, Hon. Gudaji Kazaure, ya zargi gwamnan CBN da babban bankin kasar da rike wasu makudan kudade na harajin wanda yace ya kai Naira tiriliyan 89 ba bisa ka’ida ba, zargin da ya haifar da cece-kuce a tsakanin jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here