Abu ne mai wuya Messi ya tsawaita kwantiragin sa da PSG – Rahoto

0
93

Duk da cewa alamu na nuna cewar Lionel Messi zai tsawaita kwantiragin sa da kungiyar PSG, toh sai kuma wasu rahotanni na nuna cewa dan wasan na Argentina na shirin yin kome ga tsohuwar kungiyar sa ta Barcelona.

A cewar wani marubucin labarin wasanni na kasar Spain Gerard Romero, akwai shakku game da batun tsawaita zaman Messi a PSG.

Ya ce nasarar da dan wasan ya samu ta lashe kofin duniya, ta sauya masa tunani musamman yadda yanzu ya daina fifita lamuran wasa akan wasu abubuwa.

A ‘yan makwannin da suka gabata ne dai aka fara saran dan wasan mai shekaru 35 zai cimma yarjejeniya da shugaban kungiyar Nasser Al-Khelaifi, duk da cewar a ranar 30 ga watan Yuni ne kwantiragin sa da PSG zai kare.

Toh sai dai ana ganin babbar hanyar da za ta bada damar Messi ya yi kome Barcelona ita ce rage kaso mai gwabi daga cikin albashin sa ganin halin da kungiyar ke ciki na rashin kudi.

A shekarar 2021 ne dai Messi ya bar Barcelona inda ya koma PSG suka sake hadewa da tsohon abokin wasan sa Neymar. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here