Wani dan sanda ya ki karbar cin hancin Naira miliyan 1 kan ya saki wani mai garkuwa da mutane a Kano

0
110
police
police

Wani dan shekara 62 mai suna Bamuwa Umaru, ya fada hannun hukumar ‘yansanda ta jihar Kano bisa zarginsa da kokarin ganin an sako wani mai garkuwa da mutane mai suna Yusuf Ibrahim.

Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna wanda ya sanar da hakan a jiya talata ya ce, an cafke Umaru ne yayin da yake kokarin baiwa wani dan sanda cin hancin naira miliyan daya don ya sako Yusuf Ibrahim.

Haruna ya ce, a karamin binciken da rundur ta yi kan wanda ake zargin, ya tabbatar da cewa, da hannunsa ake sace-sacen jama’a a wasu kauyuka a jihohin Katsina da Zamfara, inda kuma ya amsa cewa, tawagarsu ta masu garkuwa sun kashe wasu da suka sace 10.

Jami’an tsaro na ‘yansanda masu dawo da zaman lafiya (ORP) a karkashin jagoranci CSP Usman Abdullahi na caji ofis din Rijiyar Zaki ne suka kama Ibrahim bayan da wani direban mota da suka taba sace shi a kan babbar hanyar Funtuwa zuwa Gusau har suka karbi kudin fansa naira miliyan 500,000 ya tona masa asiri.

Kakakin ya ce, kwamishin rundunar ‘yansanda na jihar Mamman Dauda, ya nuna jin dadinsa akan goyon bayan da al’ummar jihar da kuma sauran jami’an tsaro ke baiwa rundunar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here