Majalisar dokoki ta yi barazanar kama Emefiele kan rashin bayyana a gabanta

0
103

Kakakin Majalisar Dokoki, Femi Gbajabiamila, ya yi barazanar ba da umarnin kama Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele idan ya gaza bayyana a gabanta a ranar Talata mai zuwa.

Barazanar na zuwa ne a lokacin da ke mayar da martani kan wata wasika da babban bankin ta aike kan cewa Emefiele ba zai samu damar gayyatar da majalisar ta yi masa ba.

Majalisar ta bukaci Emefiele da ya yi mata karin haske kan sabon tsarin adadin kudaden da mutane za su iya cirewa.

Wasikar da aka karanta a zauren ajalisar a ranar Alhamis, kakakin majalisar na cewa ba zai yi kasa a guiwa ba wajen amfani da sashen dokokin tsarin mulki ta 1999 wajen tilasta wa gwamnan CBN bayyana a gabanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here