Sunayen ‘yan Najeriya da suka mutu suka bar dukiya a Birtaniya

0
80

Gwamnatin Birtaniya ta wallafa jerin sunayen ‘yan Najeriya da suka mutu suka bar dukiya mai tarin yawa a kasar amma ba tare da an gano makusanta da za su gaji wannan dukiyar ba.

An ruwaito cewa, daga cikin dukiyoyin da mutanen suka mutu suka bari har da gidaje, wadanda a karkashin dokokin Birtaniya, matukar aka share tsawon shekaru 30 daga ranar mai ita ya mutu amma ba a gano magadan mamancinsa ba, dukiyar za ta zama mallakin baitil-mali.

Daga cikin mamatan da Gwamnatin Birtaniyar ta fitar da sunayesu kuma aka rasa magadansu har da wani mai suna Mark N’woko da ya rasu tun ranar 9 ga watan Disambar 1992 a garin Surrey da ke Birtaniya.

Hakazalika, akwai wani mai suna Victor Adedapo Olufemi Fani-Kayode, wanda ya mutu ranar 15 ga watan Agustan 2001 a Biermingham, to amma har yanzu ba wanda ya gabatar da kansa a matsayin dan uwa ko makusanci domin ya gaje shi.

Haka kuma a jerin mamatan, akwai Adenike Adebiyi da ya mutu a 2004; Akanni Jeremiah Adejumo da ya mutu a 2017; Solomon Adekanmibi a 2021; Richard Adesanya a 2011; Jeff Adhekeh a 2021; Isaac Ademola Adio a 2012; Julius Ajidahuan a 2009 da Julius Taiwo Akinyeye dan asalin Jihar Ondo wanda ya mutu a 1995 da makamantansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here