Turawa sun fi sonmu bakaken fata fiye da larabawa – Daurawa

0
98
Daurawa
Daurawa

Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa, alamu masu karfi sun nuna Turawa sun fi son bakaken fata fiye da Larabawa.

Daurawa ya ce, bakaken fata Musulmai na kaunar Larabawa, amma kwata-kwata su Labarawan ba wani son bakake suke ba.

A cewarsa, Larabawa sun fi nuna sha’awa da kaunar Turawa, yayin da su kuma Turawan ke tsoro da gyamar Larabawa a cikinsu.

Daurawa ya bayyana hakan ne a cikin wani gajeren bidiyon da aka yada a kafar Facebook, inda yake bayyana alaka tsakanin duniyar bakin fata Musulmi, Bature da Balarabe.

Turawa ne ke ba bakaken fata tallafi Ya kuma bayyana cewa, mafi yawan kayayyakin tallafin karatu da magani da sauran abubuwa da ake ba bakaken fata sukan fito ne daga hannun Turawa.

Duk da haka, ya ce bakaken fata kallon tallafin da ya fito daga hannun bature suke a matsayin wani shiri na kawo barna a cikin al’umma.

A kalamansa, cewe ya yi: “Mu mutanen Afrika Allah ya jarabce mu da son Larabawa amma su basu fiye sonmu da yawa ba. Kuma Allah ya jarabce mu da kin Turawa, amma kuma Turawa sun fi sonmu da son mu’amala damu da tausayinmu fiye da Larabawa a wannan zamanin.

“To za ka ga taimakon da ke zuwa mana a Afrika kaso 65% daga kasashen Turawa ne. Amma duk da haka, ko maganin Bature ne sai kaji an ce anya, wannan mugu ne fa. Ina jin abin nan fa akwai mugunta a ciki.

“Duk abin da ya fito daga Bature ko ruwan sha ne mutum sai ya tuhume shi, ko mai kyansu kuwa. Kuma sonmu suke su yi ta kashe kudi, watakil kuma ba sonmu suke ba, cutar ce basa son ta tashi ta je wurinsu, sai su tare a nan a kashe ta.”

A cewarsa, Turawa na turo kudi a gyara ilimi, a yi hanyoyi a gyara zaizaiyawar kasa da sauran ayyukan ci gaba a Afrika.

Komai Balarabe ya ba dan Afrika alheri ne, a fahimtar mutane

A cewar Malam Daurawa, mutane suna karbar dukkan abin da ya zo daga hannun Larabawa hannu bibbiyu ko da kuwa menene saboda alaka ta addini.

A bangare guda, ya ce abubuwa guda biyu ne ke sa Balarabe ya so bakin fata; iya Turanci da kuma kwallon kafa.

Ya ce abubuwan da suke fara dubawa a bakin fata ba addini ne ko wani abu ba, sun fi mai da hankali ga kwarewarsa a kwallon kafa ko kuma murda harshe a zabga turanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here