‘Yan Nijeriya da dama basu nuna jin dadinsu ba ga labarin da ya fito daga hukumomin sojojin Nijeriya na Shirin mika tubabbun ‘yan Boko Haram 613 da aka tabbatar da ba su da hatsari ga al’umma zuwa gwamnatocinsu jihohinsu na asali don ci gaba da rayuywa a cikin al’umma.
Tubabbun ‘yan Boko Haram din su 613 sun samun horo na musamman ne a kakashin shirin nan na ‘Operation Safe Corridor’.
A ra’ayin wannan jaridar, ya kamata rundunar soja ta yi takatsantsan a kan wannan shirin, dalilin mu kuma bashi da wani wahalar ganewa.
Kamar yadda muka yi tunani, shirin yana fuskantar turjiya da korafi kala-kala daga ‘yan Nijeriya. Yayin da wasu ke ganin wadannan mutane na da bukatar a sake basu dama karo a biyu, ya kuma kamata a sake tsugunar dasu a kuma mayar dasu a cikin al’umma kamar dai yadda rundunar sojen ta shirya, wasu kuma na ganin hadarin yin haka, suna masu cewa bai kamata a ba irin wadannan ‘yan ta’adda amana mai yawa ba.
Wasu mutanen kuma suna da ra’ayin cewa, watakila wasu daga cikin ‘yan ta’adda an tilasta musu shiga harkokin ta’addancin ne tunda farko, ba wai ‘yan ta’addan ne kai tsaye ba.
An gano cewa, shirin sake tsugunar da ‘yan ta’addan yana da muhimmanci wajen saffara mutanen da ake ganin ‘yan ta’adda ne don su samu damar sake shiga cikin al’umma su ci gaba da rayuwarsu kamar yadda suka saba a da can. Amma kuma yana da matukkar muhimmanci a tabbatar da daukar dukkan matakan da suka kamata don kare al’ummar da za su sake shiga cikin hatsarin da zai iya cutar da al’umma.
Bayani ya nuna cewa, yan Nijeriya da dama na da ra’ayin cewa, yawancin ‘yan ta’addar basu tuba har ciki ba, sau da yawa sukan sake komawa harkokin sun na ta’addanci bayan sun ayyana tubar su.
Idan za a iya tunawa, a shekarar 2020, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa wani dan Boko Haram da ya tuba aka kuma tsugunar da shi a sansanin sojoji, bayan ya koma gida sai ya kashe mahaifinsa ya kuma sace dukiyar mahaifin ya bace bat. Dan majalliar dattawan ya kuma kara da cewa, yawancin ‘yan Boko Haram da suka tuba tuni suka koma daji inda suke ci gaba da ayyukan ta’addancin.
Haka kuma idan za a iya tunawa a watan Yuli na shekarar 2022 wasu tubabbun ‘yan Boko Haram duk da sun ayyana tuban su amma an kama wasu daga cikin su suna tuntubar abokansu ‘yan ta’adda har ma suna basu bayanai na sirri.
Tsofaffin ‘yan ta’addar na daga cikin mutane 800 da aka sake dawo dasu cikin garin Bama na Jihar Borno aka kuma tsugunnar dasu a makarantar Mata ta garin Bama (GGSS).
Yana da matukar muhimmanci a fahinci cewa, tun da aka fara ta’addancin kashe-kashe na Boko Haram a shekarar 2009, yankin arewa maso gabas da Nijeriya gaba daya ba a samu cikakken zaman lafiya ba. Rahottanni sun nuna cewa a cikin shekara 10 kungiyar ta zabi hanyar ta’addanci da kashe-kashen al’umma inda aka tabbatar da sun kashe fiye da mutum 100,000 inda kuma suka samu nasarar tarwatsa mutum miliyan 2.5 daga muhallinsu.
Duk da ci gaba da fattakar su da rundunar sojin Nijeriya ke yi da kokarin da gwamatin tarayya ke yi a kan kungiyar har yanzu kungiyar na ci gaba da zama barazana ga zaman lafiyar al’ummar kasar nan.
A kwanakin baya muka yi tir da yadda aika saki tubabbun ‘yan Boko Haram musamman ganin ana ci gaba da yakin da ake yi dasu, muna kuma nan a kan wannan ra’ayi namu.
A ra’ayinmu, bai kamata a dauki tubabbabun ‘yan Boko Haram da wani muhimmanci ba har ana bude musu wata kofar amfana da tattalin arziki da samar musu wata dama a fagen zamantakewa kuma daida lokacin da ake ci gaba da fuskantar yakin da suka haifar wa al’umma.
Abin takaicin kuma a nan shi ne a ‘yan makonnin nan an samu karin hare-haren ta’adda dana ‘yan bindiga a daidai lokacin da Nijeriya ke fuskantar matsaloli biyu na ‘yan ta’adda dana ‘yan bindiga a sassan Nijeriya. Haka kuma a bayyana yake cewa, wasu ‘yan Boko Haram suhn rikide sun zama ‘yan ta’adda suna ci gaban da gallaza wa al’umma a yankin Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiyar Nijeriya.
A baya mun nuna rashin amincewa da shirin yi wa ‘yan ta’adda da ‘yan Bindiga da ‘yan Boko Haram afuwa ba saboda shirin gwamati na yi wa ‘yan ta’addan afuwa bai taba samun nasara ba, domin a halin yanzu wasu daga cikin ‘yan ta’addan suna can yanin Arewa maso yamma suna ayyukansu na ta’addanci da suka hada da satar shanu da kashe-kashe jama’a.
Ya kamata a fahinci cewa, tura tubabbun ‘yan ta’adda cikin al’umma wani abu ne kamar na gayyatar tashin hankali da bala’i musamman ba a samar da wata hanyar sanya ido a kan harkokinsu ba. Tuni za su koma harkokinsu na ta’addanci har ma su jawo wasu cikin ayyukansu na ta’addancin.
Yin haka ma yana zama kamar an yi watsi ne da gudanar da adalci ga wadanda suka halaka sakamkon ayukkan ‘yan ta’addar, haka kuma yana nuna kamar mutum na iya aikata komai ya kuma tsira da shi kenan, tunda ana yafe wa mutumin da ya aikata kashe-kashen dan adam.
In har ana son a tabbatar da yaki da Boko Haram yadda ya kamata tare da kare al’ummar Nijeriya dole gwanatin Nijeriya ta dauki tsatsaurar mataki na hukuta dukkan mutanen da suka aikata manya da kananan laifukka. Wannan kuma ya hada da sake tsuguar da tubabbabun a’yan Boko Haram tare da sanya ido a kan ayyukansu kafin a kai ga mayar da su cikin al’umma.
Tabbas sake mayar da tubabbaun ‘yan Boko Haram zuwa jihohinsu a sassan Nijeriya babban hatsari ne kuma ba abin da za a iya maraba da shi ba ne hakan yana kuma sanya rayuwar al’umma cikin babbar barazana ne. Dole gwamnati ta dauki karin mataki a fuskantar kungiyar da mutanen ta tare da hukunta duk wanda aka tabbatar da yana da hannu a kashen-kashen al’umma.