NIS ta kubutar da mutane 45 daga hannun masu safarar mutane a Jigawa

0
85

Hukumar da ke kula da shigi da fici ta kasa, ta ce, ta samu nasarar kubutar da mutum arba’in da biyar daga hannun masu safarar mutane a shekata ta 2022 a jihar Jigawa.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, ASI Nura Usman ya bayyana haka a wata tattauna wa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, a farkon wannan makon.

Kamar yadda ya ce, jami’an hukumar ta NIS sun gano abubuwa da dama a bincike daban-daban da suka gudanar a wannan lokacin.

An gano mutanen ne a kan hanyarsu ta zuwa kasar Tirifoli da Libiya, ta hanyar Jamhuriyar Nijar, wadanda kuma a halin yanzu an mika su ga hukumar yaki da safarar mutane ta kasa.

Kamar yadda Usman ya ce, NIS na yin shirin wayar da kan jama’a a dukkan jihohin kasar nan ta hanyar kafafen yada labarai da kuma gabatar da laccoci ga ‘yan bautar kasa da kuma mazauna gari kan hatsarin da ke tattare da hulda da masu wannan muguwar dabi’a ta yin safarar mutane.

Da yake karin haske kan kokarin da hukumar ke yi na kawo karshen safarar mutanen sai Usman ya ce, yanzu haka NIS tana gudanar da wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen rage wannan mummunan kasuwanci, sannan kuma sai ya shawarci iyaye da kada su yarda a rudi ‘ya’yansu wajen fita da su zuwa wata kasar waje.

A karshe, ya roki mazauna jihar da cewa a duk inda suka ga ana kokarin safarar mutane da su gaggauta sanar da hukumar da abin ya shafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here