Wasu jiragen sojin Indiya biyu sun yi hatsari, matukin jirgi daya ya mutu

0
92

Wasu jiragen yakin sojin saman Indiya guda biyu sun yi hatsari a yau asabar, matukin jirgin daya ya mutu, a wanan hatsarin da ya faru a sararin samaniya  a lokacin da yake atisaye a kudancin New Delhi babban birnin kasar.

Hadarin dai ya hada da wani jirgin Rasha Sukhoi Su-30, dauke da matukan jirgi biyu, da kuma Mirage 2000 da Faransa ta kera, na uku.

Dukkanin jiragen biyu sun tashi ne da safe daga sansanin sojin sama na Gwalior, mai tazarar kilomita 50 (mil 30) gabas da inda suka sauka.

A wata sanarwa da rundunar sojin saman kasar ta fitar ta ce “Jirgin na kan aikin horas da su ne na yau da kullum”, inda ta kara da cewa daya daga cikin matukan jirgin uku ya samu munanan raunuka.

Ya kara da cewa ana gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin.

Wani jami’in ‘yan sanda Dharmender Gaur ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa an samu wani matukin jirgin da ransa amma ya samu rauni a dazuzzukan Padargarh mai tazarar kilomita 300.

An umurci hukumomin yankin da su taimaka da aikin ceto da agajin sojojin sama, in ji Babban Ministan Madhya Pradesh Shivraj Singh Chouhan a shafinsa na Twitter.

Hadarin dai shi ne na baya-bayan nan a jerin hadurran jiragen sama da suka hada da jiragen sojin kasar Indiya.

Sojojin kasar 5 ne suka mutu a watan Oktoban da ya gabata a lokacin da jirginsu mai saukar ungulu ya fado a jihar Arunachal Pradesh, kusa da kan iyakar kasar da ake takaddama a kai.

Wannan dai shi ne karo na biyu da jirgin saman soji ya yi hatsari a jihar a cikin wannan watan, makonni bayan da wani jirgin sama mai saukar ungulu na Cheetah ya fado kusa da garin Tawang, inda ya halaka matukinsa.

Babban hafsan tsaron Indiya, Janar Bipin Rawat, na cikin mutane 13 da suka mutu a lokacin da jirginsa mai saukar ungulu samfurin Mi-17 na kasar Rasha ya yi hatsari a lokacin da yake dauke da shi zuwa sansanin sojin sama a watan Disambar 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here