A ranar Litinin ne za a yanke hukuncin karar da ke neman a tsige Buhari

0
87
Buhari
Buhari

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja za ta yanke hukunci a ranar Litinin, 30 ga watan Janairu, a karar da ta shigar na neman a tsige shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) daga mukaminsa bisa zargin tafka magudi a zaben shugaban kasa na 2019.

Hukuncin da mai shari’a Inyang Ekwo zai yanke zai kuma warware bukatar dakatar da gudanar da zaben shugaban kasa na 2023 da aka shirya gudanarwa a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Sanarwar yanke hukuncin da ‘yan jarida suka gani a ranar Juma’a a ma’aikatar shari’a ta tarayya da ke Abuja ta nuna cewa mai shari’a Ekwo ne zai yanke hukuncin da karfe 9 na safe.

An aika da sanarwar kai tsaye ga Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN) a matsayin Babban Jami’in Shari’a na Tarayya ga Shugaba Buhari.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Hope Democratic Party haifaffen jihar Ribas a zaben 2019, Cif Ambrose Owuru, ya kafa shari’a a kan Buhari da hukumar zabe mai zaman kanta.

Owuru, wani lauyan tsarin mulki da kasar Burtaniya ta horar da shi wanda ya zama cikakken lauya a Najeriya a shekarar 1984 amma ya bukaci babbar kotun tarayya ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Daga cikin sauran abubuwan da ya rage, ya bukaci kotun da ta jany e halascin ko akasin hukuncin da INEC ta yanke a shekarar 2019 inda ta dage zaben daga ranar 16 ga watan Fabrairu zuwa 23 ga Maris.

Ya yi ikirarin cewa INEC ta sabawa kundin tsarin mulkin kasar ta haramtacciyar hanya in da ya nemi da  a sauya zaben shugaban kasa sannan a janye bayyana Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya yi nasara ta wannan haramtacciyar hanya.

Tushen da’awar nasa ya ta’allaka ne a kan cewa karar da ya shigar a kan Buhari ba ta yanke hukunci daga kotun koli ba kamar yadda doka ta tanada.

Dan siyasar ya yi ikirarin cewa an yi watsi da karar da ya shigar a kotun kolin bisa rashin adalci sakamakon rashin halartar kotun kolin saboda sabani da aka samu a ranakun sauraron karar da aka kai masa.

Don haka ya roki kotu ta tsige Buhari ta kuma ayyana shi (Owuru) a matsayin sahihin shugaban kasa kuma a tilasta wa Buhari ya dawo da duk wasu kudaden da ya karba a matsayin albashi da na tsaro.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar HDP ya kuma bukaci kotun da ta bayar da umarnin rantsar da shi na tsawon shekaru hudu bayan tsige Buhari daga mukaminsa sannan kuma babbar kotun tarayya ta hana INEC gudanar da zaben shugaban kasa a 2023.

Yayin da ya ke ikirarin cewa shugaba Buhari ne ya kwace wa’adin mulkinsa, mai shigar da kara ya yi addu’ar Allah ya sa kotu ta tilasta wa Buhari ya dawo da duk wasu kudaden da ya karba a matsayin albashi da kudaden alawus-alawus da kuma tsaro.

A ranar 4 ga watan Nuwamba ne mai shari’a Ekwo ya sanya ranar 30 ga watan Janairu a matsayin ranar da za a yanke hukunci bayan Buhari da AGF da INEC da kuma masu kara sun amince da yin jawabi na karshe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here