Yammacin Turai za ta bai wa Ukraine jiragen yaki sama da 300

0
125

Kasashen turai sun yi alkawarin bai wa Ukraine tankokin yaki 321 a ci gaba da yakin da take yi na kare  kanta daga Mamayar Russia.

Jakadan Ukraine a Faransa Vadym Omelchenko ne ya bayyana hakan, yana mai cewa idan aka hada jimlar tankokin yakin da kasashen turawan suka yi alkawarin baiwa Ukraine zai kai adadin 321n.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Koriya ta arewa ke gargadin Amurka da ta rage karambani da rawar kai, kan abinda ya shafi yakin Ukraine da Russia gudun kar allura ta tono garma.

Duk da dai Omelchenko bai bayyana adadin tankokin yakin da kowacce kasa zata bayar ba, amma dai kawo yanzu Jamus ta sanar da bayar da nata a hukumance, bayan Amurka, Netherlands, Burtaniya, Poland da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here