Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, CGI Idris Isah Jere ya sake gargadi ga masu kunnen kashi da ke tatsar mutane kudi a ofisoshin fasfo, yana mai jaddada cewa duk wanda aka kama zai dandana kudarsa ko yanzu ko nan gaba.
Ya bayyana haka ne a yau Litinin a Legas, yayin kaddamar da ofishin tattara bayanan fasfo tare da shigar da su a manyan cibiyoyin wallafa fasfo a Alimosho da ke Legas.
“Ofishin fasfo ba wuri ne da marasa gaskiya za su iya rabuwa ba, haka nan masu ci da gumin wasu ko ‘yan ba-ni-na-iya ko kuma duk wani mutum da ba a aminta da sahihancinsa ba. Ina kara gargadin cewa doka ba za ta sarara wa duk wanda aka kama da hannu wajen aikata laifuka ko saba wa bin ka’idodjin fasfo ba kamar yadda yake kunshe a cikin dokar shige da fice, sashe na 10, karamin sashe na 1, a karkashin mataki na ‘a’ zuwa ‘h’”. In ji shugaban na NIS.
Ya yi alkawarin cewa NIS za ta ci gaba da gudanar da nagartattun ayyuka ga ‘Yan Nijeriya da suke mu’amala da su.
“NIS za ta ci gaba da aiwatar da nagartattun ayyuka ga jama’a kuma ina so na yi kira ga kowa da kowa ya rika amfani da sassan da muka samar na karbar korafe-korafe daga abokan huldarmu wadanda saboda wani dalili ko dalilai ba su ji dadin aikin da aka yi musu ba.
“Akwai wallafe-wallafe da dama, da alamomi da takardu na wayar da kai ga jama’a a kan hanyoyin da ake bi wajen samun fasfon Nijeriya. Kowa ya yi kokari ya san wadannan hanyoyin wadanda aka bullo da su na musamman domin rage katsalandan na ‘yan-ba-ni-na-iya yayin da mutum yake neman fasfo. An tsara haka ne domin magance kumbiya-kumbiyar marasa gaskiya da masu tatsar mutane kudi ko aikata abubuwan da ba su kamata ba wurin neman fasfo.” In ji CGI Idris Isah Jere.
Da yake waiwaye game da nasarorin da NIS ta samu a bangaren bayar da fasfo, Isah Jere ya bayyana cewa, “Bullo da fasfo din e-passport a shekarar 2007 ya bude wani sabon babi a tarihin aikin da aka dora wa alhakin samar da takardun tafiye-tafiye ga ‘yan kasa kamar yadda aka tanada a sashe na 2 (B) na dokar shige da fice, 2015. Kasancewar e-passport shi ne irinsa na farko a Afirka kuma na bayar wajen bayar da ingantaccen fasfo na zamani, NIS ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen bude wuraren, irin wanda Hon. Ministan yana kaddamar da aikin yau da nufin rage cunkoso na sarrafawa da bayar da bayanai a cibiyoyin fasfo tare da kawar da cunkoso.
“A yau muna farin cikin ganin yadda Hon. Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbosola ya kaddamar da wannan aiki na tarihi, manufarsa ita ce rage cunkoso a ofisoshin fasfo na Ikoyi, Festac da Alausa tare da kusantar da ayyuka kusa da ‘yan asalin karamar hukuma mafi girma a jihar Legas da kewaye.”
Har ila yau, shugaban na NIS, ya jaddada kira ga jami’an da za su yi aiki a sabon ofishin da cewa, “Ga jami’an ofishin fasfo na Alimonsho da kuka kasance na farko da za ku yi aiki a wurin, ina yi muku wasiyya da ku bai wa marada kunya, kar ku kuskura ku yi wani abin zargi yayin da kuke mu’amala da abokan huldarmu masu daraja. Ba na bukatar tunatar da ku cewa ku kasance masu ladabi da kwarewa wajen gudanar da ayyukanku. Duk wani jami’in da aka samu yana aikata abubuwan da ba su dace da doka ba zai fuskanci tsauraran matakan ladabtarwa.
“Mai girma Minista, jami’in da aka tura domin jagorantar wannan aikin na sabon ofishin tattara bayanai ya taba zama jami’in hulda da jama’a na NIS. Kafin yanzu shi ne Mataimakina na Musamman a kan Sashen Karbar Koke (SERVICOM) da kuma lashe kyautar kamubun zama Gwarzon Hukumarmu. Shi da tawagarsa a waccan sashin ne suka zama silar nasarar da aka samu daga Hukumar Kula da Saukaka Harkokin Kasuwancin Shugaban Kasa (PEBEC), a karkashin ofishin Mataimakin Shugaban kasa wanda hakan ya ba NIS damar zama mafi kyawun Ma’aikatar Gwamnati a Nijeriya tsawon watanni bakwai (7) a jere kuma wacce ta zama babbar gwarzuwa kan haka a 2022. Ya kasance daya daga cikin jami’ai biyu da tauraruwarsu ta haska a lokacin bikin karshen shekara da ba da lamobobin yabo (NIS 2022 Award/Gala Night. Ina so in tabbatar muku da cewa zai kara kwazo da kuzari da bullo da sabbin dabaru wajen mai da wannan cibiya ta zama ofishin fasfo abin koyi a Nijeriya.” In ji shi.