An kashe Fulani makiyaya 421 cikin watanni 3 a Najeriya – CPAN

0
101

Gamayyar kungiyoyin Fulani makiyaya ta Najeriya CPAN ta sanar da kisan mambobinta fiye da 400 baya ga shanunsu akalla dubu 7 cikin watanni ukun da suka gabata, lamarin da ke kara fayyace kalubalen da makiyayan ke fuskanta a kasar.

Wata sanarwa da hadakar kungiyoyin fulani 6 suka sanyawa hannu ta ce daga watan Oktoban da ya gabata zuwa Janairun shekarar nan ne aka kashe mambobin na ta su 421 ta na mai cewa galibin shanun da aka kashe wa mambobinta fiye da 7000 a wa’adin jami’an tsaro ko kuma ‘yan sintiri ne suka hallakasu a jihohin Nassarawa da Taraba da Neja da kuma Kaduna.

CPAN ta bayyana cewa kisan fulanin makiyaya na da alaka da tsananin kiyayyar da su ke fuskanta ta yadda wasu ke kallonsu a matsayin batagari ko kuma suke huce haushinsu a kansu.

Sanarwar ta koka da yadda kasuwancinsu ke fuskantar gagarumar matsala sakamakon hadaka tsakanin gwamnatin Najeriya da wasu al’ummar kasar, a kokarin shafe kabilar ta Fulani da ke sana’ar kiwo a jihohin Zamfara da Adamawa da Taraba da Benue da Pulato da Nassarawa inda matsalar ta fi tsananta a yankin kudu maso gabashin Najeriyar ta yadda ake yiwa Fulanin kisan gilla.

Gamayyar hadakar ta Fulani ta bayyana cewa daga shekarar 2017 lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya kaddamar da shirinsa na dokar hana kiwo daruruwan fulani suka fuskanci tarnakin da ya kaisu ga barin matsunansu.

A cewar sanarwar daga wancan lokaci zuwa yanzu sun tafka asarar miliyoyin dukiya yayinda ake farautarsu ba kakkautawa ake kuma kashe su tare da shanunsu a wani yunkuri na shafe kabilar daga ban kasa.

Akalla fulani Makiyaya dubu 3 suka mutu daga 2017 zuwa yanzu saboda dokar ta hana kiwo da gwamnatoci suka sanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here