Ku ba ni kwanaki bakwai zan warware matsalar karancin kudi- Buhari

0
119
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan kasar da su ba shi kwanaki bakwai domin ya warware matsalar karancin kudi da ta addabi al’umma sakamakon sabon tsarin babban bankin Najeriya.
 Ya yi wannan jawabi ne ga Kungiyar Gwamnonin APC lokacin da suka je Fadar Shugaban Kasa domin neman hanyoyin magance matsalar karancin kudi da suka ce hakan na barazana ga nasarorin da gwamnatin ke samu wajen kawo sauyi ga tattalin arzikin kasar.
 Shugaba Buhari ya ce sake fasalin kudin zai kara habaka tattalin arzikin kasar tare da samar da fa’ida na dogon lokaci yayin da ya nuna shakku kan yadda bankunan suka jajirce wajen cimma nasarar manufofin.
“Wasu bankunan ba su da inganci kawai da kansu suka damu da kansu kawai”, “ko da an kara shekara guda, matsalolin da ke da alaka da son kai da hadama ba za su bari tsarin ya tafi yadda ya dace ba.”inji Buhari
 Ya ce ya ga rahotannin irin wahalar da karancin kudaden suka sanya kananan an kasuwa da masu karamin karfi a gidajen talabijin, ya kuma ba da tabbacin nan da kwanaki 10 masu zuwa wajen magance matsaloli da wahalar da ake fuskanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here