Dan rajin kare hakkin dan adam kuma tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana tsarin canjin kudi da babban bankin Najeriya, CBN, gwamna Godwin Emefiele ya bullo da shi a matsayin bala’i da guba.
Sani ya mayar da martani ne a daidai lokacin da ake fama da wahalhalun da ake fuskanta na cire kudaden da kwastomomin bankin ke yi wanda ya kai ga yin layi a fadin kasar nan.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a kuma ya aika wa DAILY POST, Sani ya yi mamakin yadda za’ace manufofin CBN na jama’a ne amma su ka zama bala’i ga mutane maimakon zama alfanu ga jama’a.
Ya ce: “Sake fasalin kudin kasa da kuma tsarin cire kudi a ATM da Godwin Emefiele ya bullo da shi wani bala’i ne ga tattalin arziki da kuma tsari mai guba da ke da nufin saka wahalhalun Ga talakawan Najeriya i.
“Idan har da gaske gwamnatin Buhari tana son tai magnin cin hanci da rashawa, ba sai ta dau lokaci mai tsawo ba, wajen cusgunawa talakawa ba.
Tsohon dan majalisar ya bayyana cewa bankin kasa ya zama cibiyar siyasa, inda ya bayyana cewa a matsayin Najeriya na kasa mai tasowa, da manufofin tattalin arziki irin wadannan za su sa talakawanNajeriya su fahimci cewa ba ta su suke ba.
“CBN ya zama cibiyar siyasa kuma gidan miyagun tsarin tattalin arziki masu ban tsoro.
“CBN a karkashin Emefiele ya zama wurin zaman zullumi da kuma wurin kiwon fensho. Ya zama kasa a cikin wata kasar,” inji shi.
Ya kara da cewa dalilin da ya sa Buhari bai canja kudi ba musamman a shekarar 2019 da ya sake tsayawa takara ba sai yanzu?
“Me ya sa gwamnatin Buhari ba ta gabatar da canjin kudi a shekarar 2019 ba ta jira har zuwa 2023 idan manufar CBN ta hana sayen kuri’u ne?
“An mayar da Najeriya babban sansanin ‘yan gudun hijira inda jama’a ke yin layi na neman kudi a ATM. ‘Yan Najeriya sun fuskanci bala’i iri-iri da na fafutukar neman kudi a bankunan su na ajiya.
“’Yan Najeriya sun kasance suna sayen Dala a kasuwar bayan fage a baya, amma yanzu haka suna siyan Naira ta kasuwar bayan fage.
“Sanata Ahmed Lawan da ya jagoranci majalisar ya gaza wajen tantance almundahana da cin hanci da rashawa na CBN saboda gwamnati na goya masa baya. ” in ji shi