Wani mutum ya kona matarsa ​​saboda ta ki yi masa abincin dare

0
93

‘Yan sanda sun cafke Hassan Azeez dan shekaru 46 da haihuwa da laifin kona matar sa bayan ya zuba mata man fetir.
Matar mai suna Olayinka Hassan, ta bijirewa umarnin mijin nata na kai masa abinci a lokacin da ya zo gida a yunwace.

Jami’an ‘yan sanda dake hedikwatar shiyya ta Ibogun da ke karamar hukumar Ifo a jihar Ogun sun cafke Azeez bayan wani korafi da mahaifin matar ya yi  na cewa mijin nata ya kona ta kan wata ‘yar rashin jituwa da ta faru tsakaninsu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da kama Azeez.

Oyeyemi ya ce wanda ake zargin ya gudu zuwa kasar Jamhuriyar Benin tun ranar 22 ga Oktoba, 2022 lokacin da ya aikata laifin amma ‘yan sanda sun ci gaba da nemansa har zuwa ranar 22 ga watan Janairun 2023 inda daga karshe aka same shi aka kama shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here