Irin wulakancin da Vinicius Junior yake fuskanta a kasar Spain

0
203

Hukumar dake kula da gasar La Liga ta kasar Spain ta yi kakkausan suka kan yadda ake nuna tsana da cin zarafin dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Vinicius Junior.

Hakan ya biyo bayan wani butun-butumin dan wasan da aka yi na cin mutunci, wanda aka rataye a kusa da wata gada dab da filin atisayen kungiyar sannan an kuma yi rubutu a wani kyalle cewar ”Birnin Madrid ya tsani Real, wanda aka saka a jikin gadar.

Atletico Madrid da Real Madrid sun fafata a gasar Copa del Rey ranar Alhamis din da ta gabata wasan kusa da na kusa dana karshe. Sai dai Atletico ta ce wannan abin tir ne da aka aikata.

Binicius Jr dan kwallon tawagar Brazil, mai shekara 22 ya fada a baya cewar ya kamata mahukuntan La Liiga su dauki mataki kan wariya su kuma kawo karshen hakan domin tsaftace kwallon kafa.

Kafin wasan na hamayya tsakanin kungiyoyin Real Madrid a watan Satumba, wasu magoya bayan Atletico sun rera wakar cin zarafin Binicius Jr sannan sun kuma yi hakan a filin wasa na Wanda Metropolitano lokacin da za’a shiga fili a karawar da Real Madrid ta yi nasara da ci 2-1

Masu shigar da kara a Sifaniya sun ce sun kammala bincike kan wadanda suka yi wa dan wasan kalaman cin zarafi, inda suka ce da wuya a fitar da wadanda suka aikata lafin.

A farkon watan nan mahukuntan La Liga sun ce sun shigar da tuhume-tuhume da ya shafi cin zarafin dan kwallon Brazil din ga kotuna da mahukuntan. Sai dai La Liga ta ce za tsaurara bincike kan wadanda suka yi butun-butumin cin mutuncin Binicius, domin ganin an hukuntasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here