Jami’an tsaro sun yi arangama da masu zanga-zanga kan karancin Naira a Ibadan

0
97

Rahotanni daga garin Ibadan a yankin Kudu maso  yammacin Najeriya, sun ce sojoji sun harbe wani dan kabu-kabu yayin zanga-zangar adawa da karancin man Fetur da sabbin kudin Nera a unguwar Apata.

Zanga-zangar da ta gudana a manyan biranen jihar Oyo ta yi tasirin dakatar da harkokin yau da kullum, yayin da daruruwan matasa dauke da allunan da ke bayyana korafe-korafensu kan matsalolin karancin Nera da Fetur suka mamaye tituna tun daga jiya Juma’a.

Wani ganau da jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito, y ace dan babur din ya rasa ransa ne da sanyin safiyar yau Asabar bayan da aka jibge wasu sojoji a kan titi domin kwantar da tarzoma a garin na Ibadan.

Majiyar ta kara da cewar, akwai kuma wata mata da samu rauni yayin arrangamar da aka yi  tsakanin jami’an tsaron da masu zanga-zangar.

Babu dai Karin bayani a hukumance daga gwamnatin jihar ta Oyo ko kuma rundunar ‘yan sanda dangane da zargin sojojin da ake na salwantar da ran daya daga cikin masu zanga-zangar kan matsin rayuwar da ake shiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here