Najeriya na samun makudan kudade daga kashun da ake fitarwa waje – Ministan noma

0
87

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, a shekarar 2022, Nijeriya ta samu sama da dala miliyan 250 kudin shiga ta hanyar fitar da kashu zuwa kasar waje.

Ministan aikin noma da raya karkara Mohammed Abubakar ya sanar da hakan a taron masu ruwa da tsaki a fannin na noman kashu , inda ya bayyana cewa, an sa ran fannin zai kuma samar wa da manoman sa da ke aNijeriya kudaden shiga kimanin dala miliyan 500 a shekarar 2023.

Mohammed wanda ya sanar da hakan ne ta hanyar babban sakare a ma’aikatar ta aikin noma da raya karkara Ernest Umakhihe ya ci gaba da cewa, noman na kashu, na ci gaba da zama fannin amfanin gona da aka jima ana fitar da shi zuwa ketare, musamman ganin cewa, fanni ne da ke samar da dimbin kudaden shiga ga manoman kasar nan da suka rungumi fannin.

Taron na masu ruwa da tsaki wanda ya gudana a babban birnin tarayyar Abuja, ministan ya kara da cewa, an kiyasata fannin ya kai kashi 10 a cikin dari na tattalin arzikin Nijeriya, inda ya ce, wannan afanin ana noma shi a jihohin kasar nan guda 27 ciki har da babban birnin tarayyar Abuja.

A cewar ministan, ganin irin mahimmancin da fannin yake da shi, gwamnatin tarayya ta hanyar ma’aikatar aikin noma da raya karkara, ta ayyana amfanin a matsayin daya daga cikin amfanin da ke da mahimmancin matuka.

Ministan yk kara da cewa, ma’aikatar sa ta shafe shekaru ta na gudanar da ayyuka domin a kara yin noman kashu don samun riba a kasar nan, ciki har da tabar wa da manomansa ingantaccen irin na kashu.

“Ya ci gaba da cewa, kakkafa masana’antun da ake sarrafa kashu zuwa wasu nau’un abin sha a wasu jihohin da ke a kasar nan ya kara taimaka wa matuka wajen kara moman sa a kasar nan.

A cewarsa,an kima baiwa wasu manoman sa kayan fa za su yi aikinsa a honakan su da kuma horas da su akan yadda za su bunkasa sana’ar ta su.

A na sa jawabin a gurin taron, shugaban kungiyar manoman kashu na kasa (NCAN) Ojo Ajanaku ya bayyana cewa, a hankali Nijeriya na ci gaba da zama daya daga cikin kasashen da ke noman sa tare da kuma fitar da shi zuwa kasuwannin duniya.

Ajanaku ya ci gaba da cewa, wannan ya nuna cewa, Nijeriya na da kashun da zai samar wa da kasar kudaden shiga da samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar da kuma kara habaka tattalin arzikin Nijeriya.

A cewar Ajanaku, ‘yan Nijeriya fiye da miliyan uku, musamman mata tuni suka rungumi fannin na noman kashu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here