2023: Ibo mazauna Kano sun goyi bayan takarar Atiku

0
87

Al’ummar Ibo mazauna Jihar Kano sun bayyana goyon bayan su ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a babban zaɓen da za a yi a wannan watan.

Sarkin Ibo na Kano, wato Eze Ikechukwu Akpudo, shi ne ya bayyana haka a madadin al’ummar tasa a lokacin da sarkin yaƙin rundunar zaɓen Atiku a Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali-Amin (Little), ya kai masa ziyara a fadar sa.

Eze ɗin ya bayyana Atiku da cewa wani kadarko ne wanda ya yi aiki matuƙa wajen kawo haɗin kai a ƙasar nan.

Ya ce: “’Yan Nijeriya ba su da zaɓin da ya wuce Atiku, domin shi kaɗai ne wanda zai iya doke Tinubu a zaɓe. Ya na takara a babbar jam’iyya.

“Wani dalilin kuma shi ne ba za mu iya goyon bayan tsarin takarar Muslim-Muslim ba. Mu na so a samu takara mai daidaito domin tabbatar da adalci ga kowa da kowa.

“Kamar yadda ku ke gani, kwanaki kaɗan ne su ka rage kafin a yi zaɓe, amma babu wani daga cikin mu da zai tashi ya koma garin su domin yin zaɓen. A nan za mu yi zaɓen tare da iyalan mu. Nan za mu tsaya, a nan mu ke harkokin kasuwancin mu.

“Addu’ar mu ita ce a yi zaɓe cikin lumana. Mun yanke shawarar cewa Atiku Abubakar kaɗai ne zai iya tunkarar matsalolin da ƙasar nan ke fuskanta a yau.

“Mu na magana ne da murya ɗaya a matsayin mu na al’umma ɗaya. Ba mu yin wata ƙunbiya-ƙunbiya a magana, kuma mu na ba mai girma Atiku tabbacin cewa shi za mu ba ƙuri’un mu.

“Ni ɗin nan sau biyu ana zaɓa ta a matsayin kansila a Sabon Gari. Zan tattaro jama’a bakin iyawa ta don ganin Atiku ya samu nasarar lashe zaɓen da za a yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here