Girgizar kasa ta kashe mutane fiye da 500 a kasashen Turkiya da Syria

0
110

Wata kakkarfar girgizar kasa da ta afkawa kasashen Syria da Turkiya ta kashe mutane fiye da 500 baya ga rushe tarin gidaje da sanyin safiyar yau litinin dai dai lokacin da ake fargabar yiwuwar ibtila’in ya shafi wasu yankuna na tsibirin Cyprus da Masar da kuma Lebanon wadanda suka jiyo motsinta.

Sanarwar ma’aikatar lafiyar Syria ta bayyana cewa mutum 237 girgizar kasar ta kashe a iya yankunan da ke karkashin kulawar gwamnati, baya ga wasu mutum 639 da suka jikkata yayinda bayanai ke cewa a yankunan ‘yan tawayen kurdawa ibtila’in ya kashe mutane kusan 10.

Girgizar kasar mai karfin maki 7.8 ta afkawa yankunan da ke iyakar kasashen biyu ne da kuma yankunan da ke karkashin ikon gwamnatin Syria da suka kunshi Aleppo da Alatakia da Hama da kuma Tartus lamarin da ya sanya fargabar yiwuwar ta tsallaka tsibirin Cyprus da kuma Masar.

Tun da misalin karfe 4 na asubahi girgizar kasar ta dirarwa yankunan Gazantep mai yawan jama’a miliyan 2 a Turkiya inda hukumar kula da bala’o’I ta kasar ke cewa yanzu haka aka zakulo gawarwakin mutane 284 baya jikkata wasu dubu 2 da 323.

Tuni kasashen Duniya suka fara mikawa kasashen biyu tayin kai musu dauki ciki har da Amurka da ta ce a shirye take ta kawo dauki ga wadanda ibtila’in ya shafa yayinda shugaba Recep Tayyib Erdogan na Turkiya ya sanar da aike jami’ai na musamman don bayar da kulawa da kuma aikin ceto wadanda ibtila’in ya rutsa da su.

Yanzu haka dai jami’an agaji daga kasashen Faransa da Tarayyar Turai sun isa kasashen biyu don kai daukin gaggawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here