Canjin kudi da wahalar man fetur sun kai ’yan Najeriya bango

0
168

Bankin Duniya ya yi gargadi cewa muddin ’yan Najeriya suka ci gaba da fama da wahalar mai ta karancin takardun Naira, to za a shiga rashin tabbas game da babban zaben da ke tafe a kasar

Ofishin Bankin Duniya da ke Najeriya ne ya yi gargadin tare da cewa wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kudin na iya shafar tattalin arzikin talakawa da masu rauni a kasar.

Sanarwar ta ce, “Karancin takardun sabbbin kudi da ake fama da shi ya kara dagula lamurra bayan karancin mai da aka yi watanni ana fama da shi.

“Rashin takarudun kudin na barazanar jefa mutane cikin kunci wanda ke iya haddasa tarzoma, musamman yanzu da ake gab da zaben (shugaban kasa da majalisun kasa) ranar 25 ga Fabrairu da na (gwamnoni da majalisun jiha) ranar 11 ga watan Maris.

Manasa sun jaddada muhimmancin ba wa sanarwar ta Bankin Duniyan muhimanci domin tura ta kai ’yan Najeriya bango saboda ba sa iya samun kudadensu da suka samu da jibin goshi su ciyar da iyalansu.

Bankin ya ce akalla kashi 45 cikin 100 na ’yan Najeriya baligai suna da asusun banki, kashi 34 kuma na samun kudade ta hanyoyin zamani, baya ga kashi tara da suke yin sayayya ta intanet.

Babban Bankin Najeriya (CBN) dai ya sanya 10 ga watan Fabrairu a matsayin ranar daina amafani da tsoffin takarudin Naira 1,000 da N500 da kuma N200 da ya sauya wa fasali.

Wa’adi na biyu ke nan da bankin ya bayar, da karin kwana 10, bayan cikar wa’adin farko na ranar 31 ga watan Janairu.

Zargin juna kan karancin sabbin kudi

Sai dai kuma har yanzu sabbin kudaden ba su wadata a hannun ’yan Najeriya ba, lamarin da ya sa suke dogayen layuka a bankuna da injinan cirar kudi na ATM domin su samu.

’Yan siyasa dai na zargin juna kan dambarwar canjin kudin, a yayin da CBN ke zargin bankunan kasuwanci suna karkatar da sabbin kudaden da ya ba su, suna kin ba wa ’yan Najeriya.

Tuni dai tura ta kai bango a wasu wuraren inda ’yan kasa suka fara zanga-zanga kan karancin sabbin kudaden.

Lamarin ya kai ga CBN na tura jami’an tsaro suna kai samame a bankuna, inda a wasu wuraren suka bankado yadda jami’an bankunan ke boye sabbin kudaden, suna hana mutane.

A ranar Litinin Aminiya ta kawo rahoton yadda jami’an Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arzikin Kasa (EFCC) suka cafke manajan wani banki a Abuja kan zargin boye sama da Naira miliyan 20 na sabbin takardun kudaden.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here