Karancin man fetur zai sauka a mako mai zuwa – Kyari

0
147

Babban Jami’in Kamfanin Mai na Najeriya Mele Kyari, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a samu saukin matsalar karancin man fetur a mako mai zuwa.

Kyari ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da aka nuna a gidan talabijin na Channels a yammacin ranar Talata.

Sai dai ya ce ba zai iya tabbatar da cewa layukan gidajen man za su shude ba, amma ya kara da cewa za a samu ci man fetir wadatacce sosai nan da mako guda mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here