Tinubu ya bai wa iyalan wadanda ‘yan bindiga suka kashe kyautar Naira miliyan 100 a Katsina

0
101

Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da gudummawar Naira miliyan 100 ga iyalan wadanda ‘yan bindiga suka kashe a baya-bayan nan a jihar.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan a yayin taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a Katsina, ya ce gwamnatinsa na yin iya bakin kokarinta wajen ganin an kawo karshen matsalar rashin tsaro da jihar ke fuskanta.

A cewarsa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya bayar da tallafin ne domin raba wa duk wadanda matsalar tsaro ta shafa a jihar.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya gafartawa ‘yan agaji sama da 40 da ‘yan ta’adda suka kashe kwanan nan a jihar.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya tona asirin wadanda suka yi aika-aikar.

Gwamna Masari ya shaida wa taron cewa shugabanci ba abin wasa ba ne, ya kara da cewa, “Batu ne da ke bukatar mutanen da za su iya aiwatarwa.”

Ya yi kira ga jama’a da su tabbatar sun zabi APC a kowane mataki, inda ya ce jam’iyyar ta yi kyakkyawan aiki cikin shekaru bakwai da rabi na mulkinta.

“Lokacin da kuka yi wasa da jagoranci na dakika guda, za ku fuskanci sakamakon shekaru da yawa.

“Zaben 2023 yana tsakanin haske da duhu, kuma APC tana wakiltar haske.

“Damar da sauran mutane suka samu a baya, ba su yi amfani da ita wajen taimaka wa ‘yan Najeriya ba, amma kadan da muka samu, kowa ya ga abin da muka yi.

“Ba a taba samun lokacin da mata da matasa suka shiga harkar siyasa da zabe kamar yanzu ba, saboda shugaban kasa Muhammad Buhari ya kawo wasu tsare-tsare masu yawa.

“Musamman a nan Katsina an raba sama da Naira biliyan 37 a tsakanin masu karamin karfi a jihar cikin shekaru shida kacal.

“Saboda haka, ya kamata ku guji duk wanda zai yi muku karya. Ya kamata ku zabi APC a zabe mai zuwa,” in ji shi.

Gwamna Masari, ya ce da gwamnatocin baya sun yi abin da ya dace, da Nijeriya ba za ta fuskanci matsalar tsaro ba, musamman Boko Haram, satar shanu da jahilci.

A cewarsa, gwamnatocin baya sun samu dama amma sun gaza amfani da ita.

Don haka ya bukaci jama’a da kada su bari wani ya yi musu karya kan rashin tsaro ko talauci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here