Kamfanin BUA ya fara aikin hanyar Kano zuwa Kongolam

0
298

Kamfanin BUA tare da hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya ya fara aikin fadada hanyar Kano zuwa Kongolam mai nisan kilomita 132.

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola ne ya kaddamar da aikin wanda zai lashe naira miliyan 116 a garin Kazaure da ke Jihar Jigawa.

Haka kuma za a fara aikin ne daga shataletalen Dawanau a Kano, ya biyo ta Jigawa, da Katsina zuwa Kongolam.

Ministan ya ce kamfanin BUA ne ya dauki nauyin yin hanyar baki daya, a matsayin gudunmawarsa ga ayyukan raya kasa.

A nasa jawabin, Babban Daraktan, BUA Kabiru Rabiu, ya ce kamfanin zai ci gaba da hada gwiwa da gwamnati wajen aiwatar da manyan ayyukan da za su kawo ci gaba ga zamantakewa, da tattalin arzikin kasa, hadi da cigaban Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here