Kamata ya yi a daure duk dan kasuwar da ke shigo da tufafi Najeriya daga kasar waje — Dangote

0
119

Babbaan dan kasuwar nan a Najeriya da nahiyar Afirka, Alh. Aliko Dangote, ya yi wani bayani game da masu shigo da tufaafi daga kasashen waje kamar haka;

“Ga masana’antar saƙar tufafi, na yi imanin ya kamata gwamnati ta tsara doka a Majalisar Dokoki ta ƙasa da za ta sa duk wanda ya sayar da kayan saƙar tufafi na ƙasashen ƙetare da aka haramta, dole ne ya fuskanci zaman gidan yari ba tare da ba shi zaɓin biyan tara ba. Don haka za a ɗaure shi ne kawai, ko da na shekara biyu ne kawai.”

“Ainihin abun da ke faruwa a masana’antar saƙar tufafi ba tsadar wutar lantarki ba ne. Harkar saƙar tufafi ba za ta yiwu ba idan kuka ba su wuta mai rahusa amma ana ci gaba da fasa ƙwauri.”

“Abin da ke faruwa shi ne, kamfanonin ƙasashen waje suna hankaɗo da kayayyakin su Nijeriya.

“Shi ya sa ba na son shigo da kayayyaki daga kasashen waje. Lokacin da kuke shigo da kaya, kuna shigo da talauci ne tare da fitar da wadata da guraben aikin yi.” -Cewar Dangote.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here