Gwamnati na za ta gyara hanyoyin jiragen kasa domin safaran man fetur – Atiku

0
114

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha al-washin cewa a matsayinsa na dan Arewa Maso Gabas mai kuma kishin yankin zai tabbatar an dauki dukkanin matakan da suka dace wajen ganin an fara fito da ar-zikin mai da Allah ya albarkaci jihohin Bauchi da Gombe da su muddin aka zabeshi a matsayin shugaban kasa a 2023.

A cewarsa, “Shekara da shekaru ana cewa akwai mai a Arewa Maso Gabas, yanzu an dawo Bauchi da Gombe, yau ga naku dan Arewa Maso Gabas. Idan kun zabi PDP za mu tabbatar da aikin man nan an yi shi wannan karon, ba za a rufe mana rijiya a ce a’a ba na mai ba. Ina son na muku wannan alkawarin in sha Allah.”

Atiku wanda ke wannan bayanin a ranar Talata a Jihar Bauchi yayin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, da ya samu halartar dubban jama’a, kana kusoshin jam’iyyar da dama sun halarci gangamin da ya gudana a dandalin wasanni da ke jihar.

Ya kara da cewa, “Mutane su na tambaya wai shin in an debo mai din nan ta yaya za a fitar da ita, ina son na fada muku cewa za mu farfado da hanyar jirgin kasa wanda za mu yi amfani da shi ya dibi mai din nan zuwa inda duk za a kai.

Atiku ya ce kusan watanni biyu su na yawon zaga Nijeriya domin yakin zabe, am-ma ba su ga inda Allah ya nuna musu yawan mutane kamar Jihar Bauchi ba, don haka ya nuna hakan a matsayin karamci sosai da aka yi masa kuma ya misalta hakan a matsayin alamun nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here