DA DUMI-DUMI: Gwamnatin jihar Kano ta garkame wani babban kanti saboda kin karbar tsohon kudi

0
114

Gwamnatin jihar Kano, ta hannun Hukumar Kare hakkin masu amfani da Kayayyakin masarufi ta jihar kano, a ranar Lahadin da ta gabata, ta rufe fitaccen babban kantin Wellcare, saboda kin karbar tsoffin takardun Naira daga wajen kostomomin su.

A cewar mukaddashin shugaban hukumar, Baffa Babba Danagundi, an rufe babban kantin ne jim kadan bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin.

Shima da yake tabbatar da labarin, Abubakar Aminu Ibrahim, babban mataimaki na musamman ga gwamnan Kano kan kafafen sadarwa na zamani ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa an rufe babban kanti bisa umarnin Gwamna Ganduje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here