Ganduje ya amince da fara daukar fasinjoji kyauta ba kudi a motocin gwamnatin Kano

0
110

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya amince da kamfanin motocin Kanawa Bas da ya fara jigilar ‘yan jihar kyauta zuwa wurin sana’o’insu da Kasuwanninsu da Ofisoshinsu da Makarantunsu da duk wuraren al’amuransu na yau da kullum

Gwamnan ya bada wannan umurnin ne don saukakawa ‘yan jihar kan tsananin rashin tsabar kudi da ake fama dashi a fadin Nijeriya.

Ganduje wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da tsohon sakataren gwamnatin Kano, kuma daraktan yakin neman zaben jam’iyyar APC na jihar Kano a 2023, Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi ya fitar, ya ce, Kamfanin zai fara wannan jigilar ne a gobe Litinin, don haka ake umartar jama’a dasu zama masu da’a da biyayya wajen hawa wannan Motoci.

Gwanma Ganduje ne ya kaddamar da Kamfanin motocin a watannin baya da suka gabata akan farashi mai rahusa, amma shirin ya hadu da kalubale kan kayyade iyakacin titunan da mashin din adaidaita sahu zai bi, hakan ta tilastawa gwamnatin janye wannan kudiri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here