Bankuna sun bijire wa kotun koli, sun daina karbar tsoffin kudi

0
111

Alamu sun nuna bankunan kasuwanci sun shiga jerin masu kin karbar tsofaffin takardun Naira duk da umarnin Kotun Koli.

Kotun Koli ta ba da umarnin tsawaita wa’adin amfani da stoffin takardun Naira 1,000 da N500 da N200 da aka sauya  zuwa ranar Laraba, 15 ga Fabrairu inda za ta dauki mataki biyo bayan karar da aka shigar a gabanta.

Binciken Aminiya ya gano yadda wasu bankunan kasuwacin ke kin karbar tsoffin kudin daga hannun jama’a yayin da suka shiga neman canji a karshen makon da ya gabata a wasu jihohi, ciki har da Abuja.

Jihohin Legas da Abuja da Kwara da Ondo da Borno da Imo da Binuwai da Edo da Neja da Ebonyi da Ribas da Oyo da sauransu, na daga cikin jihohin da aka gano bankuna ke kaurace wa karbar tsoffin kudi.

Haka shi ma Mista Owamoyo Tolani Okolo, ya ce an ki karbar tsoffin kudin da ya kai wani banki da ke yankin Owo.

Takaddamar sabbin kudi

A yankin Abuja kuwa, daya daga cikin manajojin bankin ya shaida wa wakilinmu cewa sun rufe wasu sassan bankinsu na Zenith ne saboda rashin kudi.

Lamarin ya shafi har da gidajen mai da manyan kanti kamar yadda bincike Aminiya ya gano.

Domin kuwa wasu gidajen mai wasu sassan Abuja, da suka ha da NNPCL da ke Berger da Zone 4; da gidan man Total ke Zone 3 da dai sauransu, sun daina karbar tsoffin kudi.

Haka ma labarin yake a Jihar Borno, tuni wasu gidajen mai da kantunan zamani suka kurace wa karbar tsoffin takardun Naira.

Idan ba a manta ba, a makon jiya ne kwamitin alkalai bakwai na Kotun Kolin ta dakatar Babban Bankin Najeriya (CBN) daga haramta amfani da tsoffin kudaden kamar yadda bankin ya tsara da farko a ranar 10 ga watan Fabrairu.

Wannan na zuwa ne biyo bayan karar da gwamnonin Kogi da Kaduna da Zamfara suka shigar inda suke kalubantar matakin sauya fasalin Naira da Shugaba Muhammadu Buhari ya dauka.

Lamarin da ya jefa ’yan kasa cikin rudani, yayin da wasu ke ci gaba da karbar tsoffin kudin, wasu kuwa sun ce ba da su ba gudun kada asara ta hau su.

Tuni dai wa’adin kwana bakwai da Shugaba Buhari ya ce ’yan Najeriya su ba shi domin kawo karshen matsalar, ya kare a ranar Juma’a ba tare da labari ya sauya ba.

Masana tattalin arziki sun nuna damuwa kan karancin kudin da ake ci gaba da fuskanta a kasa duk  da Majalisar Magabata saka baki cikin lamarin.

Yanzu dai abin da ’yan kasa suka zuba ido suna jira, shi ne yadda zaman Kotun Koli zai kasance ranar Laraba dangane da karar da ke gabanata kan batun sauya fasalin Naira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here