Jami’an NIS 60 na rundunar JTF sun samu karin girma kai-tsaye a Maiduguri

0
117

CGIS Jere, ya yi musu karin girman ne a wata ziyarar bazata da ya kai sansanin rundunar hadin guiwa ta JTF da ke maidugiri a ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai jihar Borno domin kaddamar da cibiyar horas da ma’aikata da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya (IOM) tare da hadin guiwar gwamnatocin kasashen Netherlands da Switzerland da Jamus suka gina.

Jere ya bayyana farin cikinsa ganin yadda jami’ansa da ke bangaren rundunar hadin guiwar ke gabatar da ayyukansu.

Ya yi gaisuwa da yabo na musamman ga mace daya tilo a cikin runduna mai jami’ai 120, sufeta Lilian Onuoha duk da cewa ya sanar da karin girma ga dukkan kananan jami’an hukumar.

NIS

Tunda farko dai, CGI ya kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum wanda mataimakinsa ya wakilta, da kuma Shehun Borno.

A nasa jawabin, Shehun Borno ya ce yana godiya ga dukkan hukumomin tsaro a Borno, kuma yana jin dadin cewa zaman lafiya ya dawo Borno gaba daya, domin daukacin kananan hukumomin jihar 27 gaba daya babu wani labarin ayyukan ta’addanci acikinsu.

NIS

CGI Isah Jere ya samu rakiyar mataimakin Kwanturola Janar mai kula da harkokin ma’aikata, Usman Babangida da kuma kwanturolan shiyya ta C (Zone C) mai jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Gombe, Bauchi da Fulato.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here