Kotun koli za ta saurari ƙarar da aka shigar kan soke wa’adin CBN

0
119

A yau Laraba ne ake sa ran kotun ƙolin Najeriya za ta saurari dukkanin ɓangarori a ƙarar da wasu gwamnonin johohi suka shigar domin hana Babban Bankin Najeriya aiwatar da wa’adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin naira na 1,000, da 500, da kuma 200.

Gwamnatocin jihohin Kaduna, da Zamfa da kuma Kogi ne suka shigar da ƙarar, inda tun farko kotun ta bayar da umurnin jingine wa’adin daina amfani da takardun kuɗin na 10 ga watan Fabrairu, wanda bankin ya bayar a farko.

Mutane dai a Najeriya sun shiga ruɗani a kan ko za su iya ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin na naira 1,000, da 500, da 200 duk da umurnin da kotu ta bayar na jingine wa’adin na 10 ga watan Fabrairu.

Haka nan rahotanni daga wurare da dama sun nuna cewa bankuna sun daina karɓar tsofaffin takardun kuɗin, suna bayar da hujjar cewa umurni ne suka samu daga Babban Bankin na Najeriya.

Haka nan ma wasu masu ƙananan sana’o’in da dama sun daina amsar tsofaffin kuɗaɗen.

Jama’ar ƙasar na sanya ido kan abin da kotun za ta ce a zamanta na yau, wanda zai iya yin tasiri kan halin da al’ummar ke ciki na ruɗani game da ci gaba ko kuma daina amfani da tsofaffin kuɗaɗen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here