Baragurbin ma’aikatan banki ne suka jefa talakawa cikin kunci – Buhari

0
104
Buhari

Ina sane da mawuyacin halin da wasu baragurbi, marasa kishin kasa, ma’aikatan bankuna, wadanda aka dora wa alhakin aiwatar da sabon tsarin sauya fasalin kudi suka jefa ‘yan Nijeriya ciki. Na yi bakin ciki kwarai da gaske kuma ina tausayawa ‘yan Nijeriya duka kan wadannan kalubale da ake fuskanta.

Domin shawo kan wannan kalubale, na umurci babban bankin kasa CBN da ya yi amfani da duk wasu halaltattun kayan aiki da hanyoyin shari’a don tabbatar da cewa ‘yan kasa sun fahimci manufofin sauyin kudin; an saukaka musu ta hanyoyi daban-daban wurin samun sabbin takardun kudi cikin sauki sannan kuma a basu hanyar maida tsoffin kudadensu cikin asusun ajiyarsu cikin sauki.

Haka kuma, na ba da umarnin cewa CBN ya kara karfafa hadin guiwa da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa, ta yadda za a tabbatar da cewa duk wata cibiya ko wasu da aka samu sun kawo cikas ko yin zagon kasa a aiwatar da shirin sauya fasalin kudin, hukumomin su dauki doka.

A lokacin tsawaita wa’adin daina amfani da tsoffin kudaden, na saurari shawarwari masu mahimmanci daga ‘yan kasa da cibiyoyi masu ma’ana a fadin kasar nan.

Haka nan kuma, na tuntubi wakilan Gwamnonin Jihohi da Majalisar Iyaye ta kasa, a matsayina na shugaba mai mutunta doka, na bar hukuncin a hannun kotunan kasarmu kuma tuni aka fara batu kan shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here