Kotu ta tsare wani matashi kan luwadi da karamin yaro a Kaduna

0
228

Kotun Majistare da ke Kaduna ta tisa keyar wani matashi zuwa gidan yari kan zargin luwadi da wani yaro dan shekara 10.

Mai gabatar da kara, Sufeto Chidi Leo, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya yaudari yaron ne zuwa dakinsa ya yi lalata da shi.

Ya bayyana wa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne ran 22 ga Janairu a inda yake da zama.

A cewarsa, laifin ya saba wa Sasahe na 261 na kundin ‘Penal Code’ na Jihar Kaduna.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Emmanuel, ya bukaci a tura batun zuwa Sahshen Shigar da Kararraki na Jihar Kaduna domin neman shawara.

A karshe, Alkalin kotun ya dage shari’ar zuwa ran 20 ga Maris, 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here