Buhari zai mika mulki ga zababben shugaban kasa, ba gwamnatin wucin gadi ba – Garba Shehu

0
99

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu, ya karyata ikirarin cewa gwamnatin Muhammadu Buhari na kokarin ganin an kafa gwamnatin rikon kwarya, yana mai cewa babu yadda za a yi musanyan naira ya sa a ki gudanar da zabe har shugaban kasa ya zarta ranar 29 ga watan Mayu.

Shehu ya ce masu yada irin wannan jita-jita ba za su amfana da komai ba, suna haifar da fargaba da tunzura jama’a kan gwamnatin tarayya. Hakan na kunshe ne a wani bangare na sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a ta shafinsa na Twitter.

Ya kara da cewa, musanya kudin ya haifar da matsin lamba ga hukumomin tabbatar da doka da oda, da kuma jam’iyyar da zababbun jami’anta da ‘yan takara. Shehu ya kuma ce Buhari ya damu da samar da hanyoyin magance matsalar kuma ya bude hanyoyi da dama domin tuntubar shugabanni da kungiyoyi a fadin kasar nan.

Wani bangare na sanarwar ya kara da cewa: “Bari mu fito fili mu kuma jaddada cewa babu kanshin gaskiya a kan ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na kokarin kafa gwamnatin rikon kwarya ko ma mafi muni, tabarbarewar dimokuradiyya- dimokuradiyyar da ya taimaka wajen kiyayewa ba nan gida ba, har a Yammacin Afirka amma da duk faɗin nahiyar. “Shugaban kasa na fatan mika ragamar mulki ga zababben wanda zai gaje shi. Hakan zai faru ne a ranar 29 ga Mayu, 2023 kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here