CBN ya yi amai ya lashe kan ci gaba da karɓar tsofaffin naira 1,000 da 500

0
133

Babban Bankin Najeriya ya janye batun ci gaba da karɓar takardun kuɗi na N1,000 da 500, bayan a baya ya tabbatar wa BBC cewa ya umurci bankuna su ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗin.

Tun farko, Babban Bankin na Najeriya ta bakin daraktansa na yaɗa labaru, Osita Nwanisobi ya tabbatar wa BBC cewar ya bai wa bankuna umurnin ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗi na 1,000 da kuma 500.

Sai daga baya bankin ya fitar da wani takarda ɗauke da sa hannun daraktar yaɗa labarun na CBN inda yake musanta hakan.

Bayan da BBC ta sake kiran sa domin tantance bayanin, Mr Nwanisobi ya ce bai da abin da zai fada baya ga wannan sanarwa da ya fitar daga baya.

Rahotanni daga wasu jihohin Najeriya dai sun bayyana cewa an gudanar da zanga-zanga kan ƙarancin sababbin kuɗin.

A ranar Alhamis ne shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga al’ummar ƙasar, inda ya bayyana tsawaita amfani da tsofaffin takardun kuɗi na N200.

Sai dai duk da hakan wasu jihohin sun buƙaci al’umma su ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗaɗen na naira 1,000 da 500 da kuma 200.

Dama dai kotun ƙolin ƙasar ta ta buƙaci a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin har sai lokacin da ta yanke hukunci bayan ƙarar da wasu gwamnonin jihohin ƙasar suka shigar a gabanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here