Korea ta Arewa ta harba makami mai linzami mai cin dogon zango

0
102

Korea ta Arewa ta harba wani makami mai linzami mai cin dogon zango a yau asabar, in ji rundunar sojin Korea ta Kudu, gwajin farko da Pyongyang ta yi cikin makonni bakwai, wanda ke zuwa kwanaki kadan kafin a fara atisayen  hadin gwiwa tsakanin kasashen Korea ta kudu da Amurka da wasu kasashen yankin..

Rundunar Sojin Seoul ta ce ta gano harba wani makami mai linzami mai cin dogon zango da aka harba a cikin tekun gabas daga yankin Sunan na Pyongyang, da misalin karfe 17:22 agogon kasar.

Sojojin Korea ta Kudu na cikin shiri yayin da suka hada kai da Amurka tare da karfafa sa ido da kuma taka tsantsan.

Ita ma kasar Japan ta tabbatar da harba makamin, jami’an tsaron gabar tekun sun ce makamin mai linzami  ya fada a halin yanzu, ba tare da bayar da cikakken bayani ba.

Mataimakin ministan tsaro na Japan Toshiro Ino ya ce makamin ya fada a cikin tekun Japan a yankin tattalin arzikin Japan na musamman, mai tazarar kilomita 200 yamma da Oshima, Hokkaido.

A martanin da ta mayar, Seoul ta kara wani atisayen soji na hadin gwiwa tare da babbar kawarta ta tsaro Washington, a wani yunkuri na shawo kan al’ummar Korea ta Kudu da ke kara firgita a kan kudurin Amurka na dakile Pyongyang mai makamin nukiliya.

Kaddamar da shirin na yau asabar, wanda shine na farko da Pyongyang  ta yi tun ranar 1 ga watan Janairu,na zuwa ne kwanaki kadan kafin Seoul da Washington su fara wani sabon atisaye.

Shugaban kasar Korea ta Kudu, Yoon Suk Yeol, wanda ya hau karagar mulki a watan Mayun shekarar 2022, ya sha alwashin yin kakkausar suka kan Koriya ta Arewa, kuma yana kokarin kara karfafa abin da ake kira tsagaita bude wuta, wanda a karkashinsa kaddarorin nukiliyar Amurka ke ba da kariya ga kasashen yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here