Taron kungiyar kasashen Afrika karo na 36 dangane da batun ciniki bai daya

0
99

Shugabannin kasashen Afirka a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, za su soma taron kolin kungiyar tarayyar Afrika AU, domin tattauna batutuwan da suka jibanci tashe-tashen hankula a yankin Sahel da DR Congo, da kuma kokarin gaggauta kafa yankin ciniki bai daya na nahiyar.

Aiwatar da batun cinikin bai daya na nahiyar Afirka da muka sani (Zlecaf), wanda ya kamata ya hada kan mutane biliyan 1.3,da ake kyautata zaton ya zama kasuwa mafi girma a duniya.

Taron na kungiyar kasashen Afrika karo na 36, ​​wanda ya hada kasashe 55, wanda kuma za a gudanar a hedkwatar kungiyar a Addis Ababa, zai baiwa shugabanin kasashen Afrika damar gaggauta  tsarin na Zlecaf, da nufin inganta harakokin kasuwanci a nahiyar, da jawo masu zuba jari.

A halin yanzu, cinikin tsakanin Afirka yana wakiltar kashi 15 cikin 100 na jimillar cinikin nahiyar.

A cewar bankin duniya, nan da shekarar 2035, yarjejeniyar za ta samar da karin guraben ayyukan yi miliyan 18 kuma “zai taimaka wajen fitar da mutane miliyan 50 daga matsanancin talauci”. Wasu daga cikin matsaloli da ake ganin za su iya kawo cikas sun hada da bambance-bambance da ake fuskanta a nahiyar.

Dukkanin kasashen kungiyar AU, in ban da kasar Eritrea, sun rattaba hannu a kai, amma tattaunawar na ci gaba da yi mata tuwo a kwarya kan jadawalin rage harajin kwastam, musamman ga kasashe masu karamin karfi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here