Karancin kudi ba zai shafi zaben 2023 ba — INEC

0
105

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce karancin kudi da ake fama da shi ba zai shafi zaben ranar 25 ga watan Fabrairu da na ranar 11 ga Maris da za a yi ba.

Yakubu ya bayyana haka ne don kawar da damuwar da ake fama da ita na karancin Naira gabanin zaben a ranar Asabar.

Ya shaida haka ne a Abuja bayan ya ziyarci cibiyar horas da ma’aikatan wucin gadi.

An dai shiga fargabar cewa za a iya dage babban zaben kasar nan na bana ko kuma a samu kura-kurai sakamakon matsalar kudi da ake fuskanta biyo bayan canjin kudi da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi.

Idan dai ba a manta ba a kwanakin baya, Farfesa Yakubu ya jagoranci tawagar gudanarwar hukumar zuwa hedikwatar CBN, inda gwamnan CBN, Mista Godwin Emefiele, ya tabbatar wa hukumar da kudaden da ake bukata domin gudanar da zaben.

“Mun ziyarci CBN a makon da ya gabata kan batun tsabar kudi domin biyan wasu ayyuka da za mu yi a ranar zabe.

“Yawancin biyan kudi da na kayayyakin ayyuka an yi shi ne ta Intanet.

“Amma akwai wasu ayyuka masu mahimmanci wadanda za a biya da tsabar kudi; kuma shi ya sa muka je CBN kuma kadan ne na kasafin kudin.

“Babban bankin kasar nan ya tabbatar mana da cewa ba za mu fuskanci wani tsaiko ba dangane da hakan. Don haka babu wata matsala dangane da hakan,” in ji shi.

Shugaban na INEC ya bayyana cewa hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar Asabar 25 ga Fabrairu, 2023.

Yakubu, wanda ya bayyana jin dadinsa da ci gaban da aka samu kawo yanzu, ya ba da tabbacin cewa a wannan lokaci a mako mai zuwa, ‘yan Nijeriya za su kada kuri’a a rumfunan zabe sama da 176,000 domin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.

Ya kuma ce za a kuma bayyana zabin da ‘yan Nijeriya suka yi na zaben shugaban kasa a Abuja.

Dangane da halin da ake ciki na tsaro a kasar nan, ya ce zanga-zangar da ake yi kan karancin kudi lamari ne na tsaro, wanda za a tattauna da hukumomin tsaro.

Ya ce jami’an tsaro sun bai wa hukumar tabbacin shirinsu na tabbatar da tsaro a duk fadin kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here