Na yi imani Tinubu zai dora daga inda na tsaya – Buhari

0
100

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci ‘yan Najeriya da su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi dan takarar jam’iyyarsa ta APC a zaben shugaban kasa da zai gudana a ranar 25, ga Fabarairun nan.

Shugaba Buhari ya yi wannan kiran ga ‘yan Nijeriya ta hanyar wallafa sakon a shafinsa na kafar sada zumunta na Facebook a yammacin ranar lahadin nan.

Shugaba Buhari yabayyana cewa, “Zuwa ga ’yan Najeriya, ina so in yi amfani da wannan dama domin in sake gode muku da kuka zabe ni har na zama shugaban kasa har sau biyu a jere.”

“A yanzu ni ba dan takara ba ne a wannan zaben, amma jam’iyyata ta APC tana da dan takara wato, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu,”

“Kamar yadda na ambata a baya, Tinubu mutum ne amintacce kuma mai gaskiya mai son Nijeriya, da kaunar ci gaban Jama’a da kasarmu,”

“Ina kira gare ku da ku zabi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Saboda mun gamsu da shi kuma na yi imani zai dora kan irin nasarorin da muka samu,”

“A karshe ina kara tabbatar muku da cewa ina da cikakkiyar masaniyar irin wahalhalun da kuke fuskanta a halin yanzu sakamakon wasu cikin manufofin gwamnati da ake aiwatarwa a yanzu da nufin kawo ci gaba a kasa baki daya,”

“Ina rokon ku da ku kara hakuri yayin da muke daukar matakan da suka dace don rage wahalhalu. In sha Allahu za a samu alheri a karshen lamarin.” a cewarsa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here