Sake fasalin Naira: Ojukwu bai yi rabin abin da El-Rufai ya yi ba – Omokri

0
98

Wani tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri, ya bayyana kaduwarsa yadda gwamna Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna ke ci gaba da yawo cikin walwala kuma har yanzu yana rike da ofishinsa bayan ya bijirewa umarnin namanufar gwamnatin tarayya na daina karbar tsohon kudi.

A ci gaba da bijirewa umarnin gwamnatin tarayya na hana tsofaffin takardun kudi na N500 da N1000, El-Rufai a ranar Lahadin da ta gabata, ya umarci ma’aikatu da hukumomi da su ci gaba da karbar tsohin kudi a dukkan ma’aikatu, har sai kotu ta yanke hukunci.

Muyiwa Adekeye, mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, a cikin wata sanarwa ya ce mutane za su iya biyan kudi ta hanyar amfani da duk wani nau’i da suka hada da naira 1,000 500.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan El-Rufai ya bukaci mazauna jihar da su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun naira. Umarnin nasa na zuwa ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana a kafar yada labaran sa na kasa cewa duka tsofaffin takardun Naira 1,000 da kuma N5,000 sun gama aiki.

Sai dai a jawabinsa ga al’ummar jihar Kaduna, El-rufai ya bukace su da su tashi tsaye wajen tabbatar da dimokuradiyya da zaman lafiya da hadin kan kasa. Shi kuma Reno Omokri a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi ya ce, “Shin Ojukwu ya aikata abin da El-Rufai ya yi lokacin gwamnatin mulkin soja ta Janar Gowon da ta kai masa hari?

“Ojukwu bai fitar da Fam na Biafra ba sai ranar 29 ga Janairu, 1968. Duk da haka, Najeriya ta matsa masa. Me ya sa Najeriya kasata ba za ta yi hakan ga El-Rufai kan cin amanar kasa ba?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here