Yadda gobarar tanka ta kona gidaje da dukiya a Ondo

0
112

Wata tankar mai dauke da fetur lita 33,000 ta kama da wuta bayan da ta fadi a yankin Idanre a Jihar Ondo.

Aminiya ta kalato cewa iftila’in na ranar Asabar ya auku ne a lolacin da direban tankar ya yi kokarin kauce wa manyan ramukan da hanyar yankin ke fama da su.

Shaidu sun ce tankar ta karkace ne ta fadi inda man da take dauke da shi ya malale a kan titi wanda daga bisani wuta ta kama.

Sun ce gobarar da tankar ta haddasa ta lalata yankin har da gidaje da dama da ke kusa.

“Gidaje da dukiya masu yawa sun kone sakamakon gobarar, mun yi kokarin agazawa a kwashe kayansu amma abin ya faskara.

“Mutane da da yawa sun shiga alhini ganin yadda kayayyakinsu ke ci da wuta saboda sakacin direban tankar,” in ji wani ganau.

Wani bidiyon gobarar da aka yada ya nuna yadda matasan yankin suka ba da gudunmawarsu wajen kokarin kashe wutar gabanin isowar jami’an kwana-kwana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here