An kama mutane 15 kan laifin fasa banki a Akwa Ibom

0
92

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Akwa Ibom ta sanar da kama wasu mutum 15 bisa zargin kai hari bankuna a Karamar Hukumar Oron a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Odiko MacDon ne ya tabbatar wa manema labarai kamen a Oron ranar Lahadi.

“Mun samu labarin cewa an kai wa wasu bankuna hari a Karamar Hukumar Oron kuma nan take ‘yan sanda suka kai dauki.

“Mutum 15 sun shiga hannu kuma ana gudanar da bincike a kan su,” in ji MacDon.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya ruwaito cewa wadanda ake zargin sun kai wa bankunan hari ne a ranar Juma’a lokacin da wasu matasa suke yin zanga-zanga kan karancin kudi.

“Kwamishanan ‘yan sanda, Mista Olatoye Durosinmi ya bayyana bakin cikinsa game da lamarin, ya kuma umarci jami’an ‘yan sanda na shiyya-shiyya a kananan hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da cewa ba a sake samun tabarbarewar doka da oda ba.”

MacDon ya kara da cewa, kwamishinan ya yi kira ga mazauna yankin da su kasance masu bin doka da oda domin duk wanda aka kama yana barnata dukiyoyin jama’a zai fuskanci fushin doka.

Ya ce rundunar ‘yan sandan za ta yi duk mai yiwuwa don ganin cewa Akwa Ibom ta ci gaba da kasancewa daya daga cikin jihohin da suka fi samun zaman lafiya a Najeriya.

Mazauna yankin sun shiga firgici sakamakon yadda zanga-zangar ta rikide zuwa tarzoma.

Wata majiya a yankin ta ce akalla bankuna uku ne aka lalata yayin zanga-zangar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here