Buhari ya nemi afuwar ’yan Najeriya kan karancin takardun kudi

0
104

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake neman afuwar ‘yan Najeriya yayin da gwamnati ke daukar matakan da suka dace don saukaka wahalar da canjin kudi ya haifar.

Ya yi wannan bayani ne a ranar Lahadi a wani faifan bidiyo da ya aiko gida daga birnin Addis Ababa na Kasar Habasha a ranar Lahadi.

A sakon, Buhari ya jaddada goyon baya ga dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu a zaben da ke tafe ‘yan kwanaki masu zuwa.

Ya kuma bukaci Sarakunan Gargajiya da Malaman Addinai da ‘yan siyasa da su gargadi mabiyansu kan tada tarzoma a lokacin zabe.

“Ina so na tabbatar muku da cewa gwamnati ta dauki kwararan matakan tsaro domin bai wa kowa damar fitowa ya kada kuri’arsa. Don haka ina kira ga kowa da kowa da a ba shi goyon bayan da ya dace.

“Yan uwana ‘yan Najeriya, ina so na yi amfani da wannan dama domin in sake gode muku da kuka zabe ni na zama shugabanku har sau biyu.

“Ni ba dan takara ba ne a wannan zabe da za a shiga ba, amma jam’iyyata ta APC tana da dan takara, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

“Kamar yadda na ambata a baya, Tinubu mutum ne mai gaskiya kuma mai son jama’a da ci gaban kasarmu.

“Ina kira gare ku da ku zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Ina da yakinin cewa zai dora daga kan nasarorin da muka samu.

“A karshe ina so na sake tabbatar muku da cewa ina da cikakkiyar masaniya game da irin wahalhalun da kuke fuskanta a halin yanzu sakamakon wasu manufofin gwamnati da ke da nufin kawo ci gaba ga kasa baki daya.

“Ina kira da ku kara hakuri yayin da muke daukar matakan da suka dace don saukaka wahalar da ake fuskanta. In sha Allah za a ga alfanun tsarin a nan gaba.”

Wannan dai na zuwa ne bayan wani taro da Kwamitin Gudanarwar APC na kasa ya gudanar a ranar Lahadi.

Taron wanda gwamnoni da Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu suka halarta, ya mayar da hankali kan batun canjin kudin da Gwamnatin Tarayya ta yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here