Akalla mutane 11 ne suka mutu yayin da dubu 6,400 suka bata a sanadin mahaukaciyar guguwar Cyclone Gabrielle a yankin Kudancin NewZealand.
Tun ranar 12 ga watan da muke ciki na Fabrairu ne guguwar ta afkawa kasar, lamarin da ya haddasa ambaliyar ruwa mai muni.
Prime ministan kasar Chris Hipkings ya kwatanta guguwar a matsayin babban bala’i mafi muni da kasar ta gani a wannan karni.
A cewar sa akwai yiwuwar samun Karin mutanen da suka mutu, la’akari da yawan mutanen da suka yi batan dabo sanadin guguwar.
Chris Hipkins ya ce guguwar ta shafi rayukan al’umma kai tsaye, yayin da har yanzu ta ki bada damar da za’a fara aikin ceto da lalubo wadanda suka bata, sai yadda guguwar ta lalata hanyoyin sadarwa, turakun wutar lantarki, da gurbata ruwan sha tare da lalata hanyoyi, yayin da ambaliyar ruwa ta shafe wasu yankunan.